Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, MDD a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Laraba danagne da kasar Burundi, ya lura cewa kodashike al’amura sun dan daidaita ta fuskar tsaro a kasar,kwamitin ya sake nuna damauwarsa kan yanayin siyasa a Burundin, da tafiyar hawainiya kan shawarwarin sulhu tsakanin al’ummar kasar a karkashin jagorancin kungiyar raya tattalin arzikin kasashe dake gabashin Afirka, da kuma rashin katabus na gwamnati ta wannan fuska.
Kwamitin ya yi marhabin lale ga sanarwar da shugaba Nkurunziza ya bayar cewaba zai nemi sabon wa’adi ba a shekara ta 2020, wadda kwamitin ya ce ana daukar matakin a zaman takun farko na rage zaman dar dar ta fuksar siyasa. Kwamitin ya ce ana bukatar ganin wasu matakai da zasu nuna cewa za’a gudanar da zabe sahihi a kasar.
Wakilan kwamitin sulhun sun yi marhabin lale tare da bayyana goyon bayan su ga sabuwar dukufa daga kungiyar hada kan kasashen Afirka AU da kuma ta raya arzikin kasashen da suke gabashin Afirka da ake kira (EAC) a takaice na ganin an warware rikicin siyasar Burundi cikin ruwan sanyi ta wajen gudanar da shawarwarin sulhu da za su kunshi dukkannin ‘yan kasar tare da la’akari da yarjejeniyar da aka cimma a Arusha ranar 28 ga watan Agustan shekara ta 2000, da kuma ta amfani da tsarin mulkin Burundi.
Haka nan kwamitin sulhun ya sake nanata goyon bayansa na aiwatar da shirin sulhun karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa B. Mkapa, da shiga tsakani da shugaba Yuweri Museveni yake yi.
Wakilan kwamitin sulhun sun sake nanata matukar damuwarsu dangane da kara tabarbarewar yanayin rayuwa data shafi kusan mutane dubu dari da tamanin, da suka rasa muhallansu amma har yanzu suke cikin kasar, da mutane milyan uku da dubu dari shida wadanda suke da bukatar a tallafa musu, da kuma ‘yan kasar kusan dubu dari hudu dake zaman gudun hijira a kasashen dake makwaftaka.
Kwamitin ya yabawa kasashe da suka karbi wadannan mutane, kuma suka ce kasashen su tabbatar da cewa, komawar mutanen zuwa Burundi ya kasance abu ne da suka nuna sha’awa wanda kuma ba zai shafi lafiya da rayuwar su ba.
Facebook Forum