Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Burundi Ta Dakatar Da Muryar Amurka Da BBC


Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza

A yayin da gwamnatin kasar Burundi ke shirin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar, ta kakaba takunkumi ga kafafen labaran Muryar Amurka da BBC har sai bayan kammala kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a game da kuri'ar.

Kasar Burundi ta yi shelar dakatar da gidajen rediyon Muryar Amurka da BBC daga yada labarai a kasar na tsawon watanni shida, makwanni biyu gabanin kada kuri’ar jin ra’ayin jama’a da za a yi a kasar kan batun kwaskware Kudin tsarin mulkin kasa, ciki har da batun canza tsawon wa’adin Shugaban kasa.

Hukumar Kula da yada labaran kasar ta Burundi, wadda ta zargi Muryar Amurka da BBC da saba ka’idar yada labarai, da kuma gudanar da wasu abubuwan da ta kira “haramtattun harkoki,” ita ce ta sanar da wannan takatarwar. Sanarwar ta ce takatarwar za ta fara aiki ne daga jibi Litini.

Hukumar ta kuma yi gargadi ga gidan rediyon Faransa (RFI), wadda ta zarga da bayar da rahotannin karya kan yiwuwar a yi bita-da-kulli ga masu kiran da a kada kiuri’ar rashin amincewa.

A wata takardar sanarwa ta jiya Jumma’a, Shugabar Gidan Rediyon VOA Amanda Bennet, ta yi tir da wannan mataki da Hukumar kula da yada labaran kasar Burundi ta dauka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG