Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miliyoyin Mutanen Kasar Burundi Dake Afrika Ta Gabas Na Jefa Kuri’a A Yau


Miliyoyin mutanen kasar Burundi dake Afrika ta Gabas na jefa kuri’a a yau a wani zaben da ake jin zai iya tsawaita mulkin Shugaba Pierre Nkurunziza har tsawon wasu shekaru 16 daga yanzu, izuwa shekarar 2034.

Mutane da dama sun tsaya a cikin dogayen layukka dake wajen rumfunan zabe a birnin Bujumbura da kasar baki daya domin kada kuri’un su.

Wa'adin mulkin shugaban kasar a yanzu na shekaru biyar-biyar ne amma kwaskwarimar da ake son yi wa kundin tsarin mulkin zata baiwa shugaban karin shekaru bakawi akan karagar mulki. Kudin Tsarin mulkin kasar ya baiwa kowanne shugaba wa’adin mulki 2 ne kawai, amma ana ta ganin cewa sauya dokar zai baiwa Nkrunziza damar ya sake tsayawa zabe har sau biyu nan gaba.

Shi dai shugaba Nkurunziza wanda tun shekarar 2005 yake kan karagar mulki, an sake zaben shi a karo na uku a shekarar 2015, abinda ya saba wa dokar da ta tanadi yin mulki sau biyu kawai. Wannan matakin yana cikin yarjejeniyar da aka rattaba wa hanu don maido da zaman lafiya a shekarar 2000 wanda ya kawo karshen mummunar yakin basasa da aka yi a lokacin, wanda akalla mutane 1,200 suka rasa rayyukan yayinda wasu mutanen Burundi fiyeda 400,000 suka yi gudun jijira daga kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG