Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD: Ta Bukaci Masu Fafatawa Su Samarda Hanyar da Kayan Agaji Zasu Kaiga Masu Neman Taimako


 Ban Ki-moon, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya
Ban Ki-moon, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya gayawa duk bangarorin da ke yaki a Syria, da su yi gaggawar samar da hanyoyin da za a ratsa da magunguna da kayan abinci, domin kaiwa ga wadanda su ke bukatar taimako.

Mambobin kwamitin su 15 suka nuna amincewarsu ta bai-daya a jiya Talata,inda suka nuna fushinsu kan yadda bangaroroin da ke fada a kasar suka yi bris da bukatan da Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar game da yakin na Syria da ke kara kazancewa.

Wannan kira na kwamitin, an yi shi ne domin gwamnatin Syria da kungiyar IS da Al- Nusra Front da kuma da kuma mayakan da ke da alaka da kungiyar Al Qaeda.

Har ila kwamitin sulhun, ya yi Allah wadai da ayyukan azabtarwa da kisa da kuma batan mutane da sauran laifukan yaki da ake zargi na faruwa a kasar, ciki har da na cin zarafin kananan yara.

A farkon jiya Talata, shugaban Majalisar Dinkin Duniya a ofishin Majalisar da ke Geneva, Michael Moller, ya ce za a yi wani zama domin tattauna rikicin Syrian a wata mai zuwa, ba tare da ya ambaci takamaimain ranar da za yi zaman ba.

Amma ya ce mai yuwuwa a yi zaman a karshen watan Janairu mai kamawa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG