Babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai a cikin firar da yayi da wata kafar talibijan kasar waje yace mayakan Najeriya sun gama da Boko Haram.
Amma wata kungiyar dake bin digdigin rigingimu a nahiyar Afirka SDM Intel tace bisa abun dake faruwa a yankin arewa maso gabashin Najeriya daga watan Janairu zuwa yanzu kimanin fararen hula dari biyu ne 'yan Boko Haram suka hallaka cikin hare hare fiye da 42. Saboda haka ba'a gana dasu ba.
Su kuwa mutanen yankin arewa maso gabas sun ce adadin hare haren ya fi 42 kamar yadda Mutari Yerima sarkin Baburawa ya shaidawa Muryar Amurka.
Yace "ko kadan basu gama da su ba. Ko wata guda ba'a yi ba 'yan Boko Haram sun fara ba mutane sanarwa a wasu kauyuka suna gargadin mutanen su tashi" Yana mai cewa daga watan Janairu zuwa yanzu an kai hari 286. Injishi an hana mutane noma amma kullum ana maganar wai an gama dasu. Acewarsa kullum mutane na mutuwa sanadiyar 'yan Boko Haram.
Lokacin azumi kafin a yi sallah akwai ranar da suka kai karfe tara basu sha ruwa ba a Maiduguri. Yace da kyar aka fatattakesu.
A can hedkwatar sojojin Najeriya babban hafsan hafsoshin baya gari. Sai dai Manjo Janar Irabor ya hakikance cewa abun da ake gani yanzu burbudin 'yan ta'addan ne amma an karya karfinsu.
A saurarin rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani
Facebook Forum