Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mazauna Yankunan Jihar Zamfara Na Ci Gaba Da Kokawa Kan Matsalar Tsaro


Yan Bindiga
Yan Bindiga

Kalubalen tsaro a Nigeria na ci gaba da zama babbar matsala da ke addabar al’ummomi musamman a yankin Arewa Maso Yammancin Kasar, inda ‘yan bindiga ke ci gaba da cin karensu babu babbaka, duk da cewa hukumomin tsaro da mahukunta na cewa ana samun nasara kan ‘yan bindigar.

Mazauna yankunan karkara a jihar Zamfara musamman a bakin iyakar jihar da Kebbi, sun koka tare da neman dauki daga hukumomi akan barnar da suka ce ‘yan bindiga na yi musu ta hanyar kona amfanin gonakinsu.

A hirar shi da Muryar Amurka, shugaban ‘yan banga a wani gari da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, Alhaji Aliyu Chairman, ya ce ‘yan bindigar sun yi gayya ne don lalata amfanin gonar al’umma, da kama manoma don neman kudin fansa, tare da sanyawa wasu mazauna yankin haraji idan suna so su zauna lafiya.

Alhaji Aliyu ya kuma bayyana cewa, yankin da ya kunshi kauyukan Zargada, Farar Ruwa, da Dan Gwadabe da ke makwabtaka da jihar Kebbi, na fuskantar matsalar karancin jami’an tsaro da zasu kai musu dauki.

Wani manomi da ke garin Wanke a karamar hukumar mulkin Gusau, ya ce ya zama dole su mika wuya saboda ba sa samun wani dauki daga jami’an tsaro.

“A takaice mu fa kamar ba a Najeriya mu ke ba. Za a azo a sanya maka kudi kuma dole sai ka bada idan kana so ka debi kayan gonarka. Yanzu akwai garuruwa kusan goma da aka sanya wa kudi kuma dole su biya kudin.”

Mustapha Jafaru Kaura, babban jami’i na musamman ga gwamnatin jihar Zamfara kan hulda da kafafen yada labarai, ya ce gwamnatin jihar na kokari matuka don ganin an samu ingantaccen tsaro.

Tuni dai mai ma magana da yawun rundunar sojan saman Najeriya Air Commodore Olusola Akinboyewa, ya ce sojojin Najeriya da ke aiki a karkashin sabuwar rundunar yaki da ‘yan bindiga a Arewa Maso Yammacin kasar sun soma fatattakar ‘yan bindigar da ke jihar Zamfara a karkashin wani aiki da suka yi wa lakabi da “Farautar Mujiya.”

Matsalar tsaro da ake fama da ita musammana a yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya, Ta zama wani abin alakakai ga al’umar yankin, duba da yadda al’umma ke ci gaba da kokawa yayin da su kuma mahukuntan kasar ke cewa ana samun nasara wajen magance matsalar.

Saurari rahoton Abdulrazak Bello Kaura:

Mazauna Yankunan Jihar Zamfara Na Ci Gaba Da Kokawa Kan Matsalar Tsaro
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG