Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ku Kamo Min Bello Turji Duk Inda Yake – Ministan Tsaro Badaru


Ministan tsaron Najeriya Badaru Abubakar
Ministan tsaron Najeriya Badaru Abubakar

Kalaman Badaru sun zo ne makonni uku bayan Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa kwanakin Turji sun kusa karewa.

Ministan Tsaro, Muhammed Badaru, ya umarci dakarun Najeriya karkashin “Operation Fansar Yamma” da su kamo shugaban ‘yan ta’adda da ake nema ruwa a jallo, Bello Turji.

Umarnin na Badaru na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da Shugaba Bola Tinubu ya yi garambawul ga majalisar ministocinsa.

Kalaman Badaru sun zo ne makonni uku bayan Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa kwanakin Turji sun kusa karewa.

Yayin da yake jawabi ga sojoji a hedikwatar Runduna ta Daya da ke Gusau, Jihar Zamfara, a ranar Alhamis, Badaru ya kara wa sojoji kwarin gwiwa, yana mai cewa Shugaba Bola Tinubu yana bibiyar ayyukansu a watannin da suka gabata kuma ya ga ci gaba mai kyau.

“Ina da tabbaci daga kwamandan sojoji kuma na ji dadi, na tabbata za mu cimma burinmu. Kuna shirye ku gama da su? Kuna shirye ku kawo karshensu? Don Allah ku kawo min Turji.” Badaru ya ce kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Badaru ya kai ziyarar ta Gusau ne da nufin samun bayanan kan yadda ake tafiyar da ayyukan soji a yankin da ‘yan bindiga suka addaba.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Yadda Tsofaffi Ke Fama Da Lalular Yanar Ido A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Fim Da Aka Shirya Kan Leah Sharibu Ya Samu Lambar Yabo
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Kalubalen Da Masu Fama Da Lalurar Galhanga Ke Fuskanta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Tasirin Cibiyar Kula Da Lafiyar Mata Da Yara Ta HopeXchange A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG