Rashin cimma matsaya kan shata wani wuri a matsayin iyakan da ya raba tsakanin kasashe ko jihohi shine makasudin samun rikice rikicen kan iyakoki a fadin duniya inda a wassu lokutan yana kaiwa ga haddasa fadace fadace a kasashen duniya ko kuma jihohi. A wani kaulin kasashe kan shigar da kara babban kotun duniya kamar yadda kasar Kamaru ta shigar da kara gaban kotun duniya a shekarar 1994 tsakanin ta da Najeriya a kokarin ta na kaucewa yaki akan tsibirin Bakassi wanda daga karshe kotun duniyar ta mallakawa kasar Kamaru tsibirin na Bakassi.
A wani bangaren kuma jihohi ma sukan shirya tarurruka tsakanin jihohi masu makwabtaka da juna don yin nazari kan matsalolin kan iyakokin su domin kaucewa tashin tashina da ka iya tasowa tsakanin al’umomin da suke zaune a kan iyakokin nasu.
A dalilin haka ne ya sa Jihar Bauchi tare da hadin gwiwar hukumar shata kan iyakoki na kasa a Najeriya ta shirya wani taron da ya gudana a jihar inda aka yi bayani kan yadda suka hada iyakoki da jihohi 7 da jihar ta Bauchin take makwabtaka da su. Wadannan jihohi sun
kunshi Jihar Gombe, Jihar Taraba, Adamawa, Yobe, Kaduna, Filato da kuma jihar Kano.
Mataimakan Gwamnonin wadannan Jihohin sun halarci taron inda wakilin Muryar Amurka a jihar Bauchi Abdul-Wahab Muhammad ya nemi sanin abin da suka fahimta akan taron da mahimmancin sa.
A latsa nan don a saurari rahoton Abdul-Wahab Muhammad:
Dandalin Mu Tattauna