Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mazauna Daga Arewa Maso Gabas Sun Kai Kukansu Abuja


Makiyaya
Makiyaya

Sabili da yadda makiyaya ke bata masu gonakansu ba tare da wata gwamnati ko ta karamar hukuma ko ta jiha ta yi wani abu ba a duka fadin arewa maso gabas, mazauna karkara a shiyar sun kai kokensu Abuja

Wata tawagar mazauna karkara daga arewa maso gabas dake fuskantar matsalar tsaro ta ziyarci ofishin Muryar Amurka dake Abuja da budaddiyar wasika dake kiran shugaba Jonathan da ya fadada ayyukan yaki da ta'adanci a wurinsu.

Shirin tsaron da suke so a fadada yakamata ya hana hudawa dake fantsamawa cikin gonaki suna barin dabbobinsu su cinye anfanii gona tare da barazana ga rayukan manoma.Maso korafin sun ce hudawan na fadawa gonaki a yankin kudancin Borno zuwa Dadin Kowa a jihar Gombe kana su mike zuwa Taraba ko Adamawa.

Da aka tambayesu dalilinsu na tsallake gwamnoni kananan hukumomi da na jihohi suka nufi Abuja kai tsaye domin mika kokawarsu zuwa fadar shugaban kasa kakakin tawagar tsohon dan majalisar dokokin Gombe Ustaz Yunus Ahmed Isa ya ce zamanin gwamnatin da ta shude an san hudawa suna zuwa. Gwamnatin lokacin ta yi iyakacin kokarinta.A zamanin mulkin Haruna Goje na shekara takwas an yi maganin hudawan. Amma bana sai hudawa suka dawo dabbobinsu na cinyewa talakawa anfani gonakansu. Yawancin gonakin dake kananan hukumomi a jihar Gombe duk sun rasa gonakansu.

Tun da gwamnatin yanzu ta yi ki yin komi shi ya sa suka kira taron domin su mika kokensu ga gwamnatin tarayya. Idan kuma gwamnatin tarayya ta ki to su dama suna jam'iyyar APC ne. Zasu kira talakawa su yi masu alkawarin cewa idan sun kafa gwamnati zasu yi maganin hudawa. Shi ma Malam Umar Boltingo ya ce hudawan sun lamushe masa anfanin gona. Ya ce da suka shigo gonarsa sun tarar da yaransa hudu suna aiki kuma duk yaran suka saresu tare da yi masu harbi ba baka. Yanzu suna kwance a asibiti. Domin gudun karya doka basu mayar da martani ba suna jiran su ga abun da gwamnati zata yi.

Mai taimakawa gwamnan Gombe kan harkokin labaru Junaidu Usman Abubakar ya c
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG