Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin Kasashen NATO Na Tattaunawa Kan Shigarsu Libiya

Wani jirgin ruwan daukar jiragen saman yakin Farasan da ake amfani da shi a yakin Libiya.
Wani jirgin ruwan daukar jiragen saman yakin Farasan da ake amfani da shi a yakin Libiya.

Ministocin kasashen Waje na kasashen da ke kungiyar tsaro ta NATO, na taro a birini Berlin don tattauna salon fafatawarsu a Libiya, a daidai lokacin da mayakan ‘yan tawaye k eta kiraye-kirayen NATO ta kara taimaka masu farmakin jiragen sama.

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton za ta hadu da takwarorinta na NATO a birnin Berlin don tattaunawa ta kawana biyu da za a fara daga yau Alhamis.

An sami rarrabuwar kawuna tsakanin mambobin kugiyar kan ko a kara kaimi wajen farmakin da ake kai wa kan dakarun Gaddafi ko a’a. Da Burtaniya da Faransa yin bukaci da kungiyar ta kara kaimin farmakin, a sa’ilinda kuma Amurka ta takaita rawar da ta ke takawa.

Taron na Berlin ya zo ne kwana guda bayan da kwamitin tuntuba na kasa da kasa ta hadu da Amurka da Tarayyar Turai da Kasashen Larabawa, su ka yi alkawarin karin gudunmowar kudi da ta siyasa ga ‘yan tawayen Libiya a taronsu na birnin Doha.

Wani kakakin ‘yan tawayen Libiya mai suna Mahmoud Shamman ya gaya wa masu halartar taron cewa kungiyar tsaro ta NATO ba ta daukar isasshen matakan kare fararen hula. Ya kuma bukaci da Amurka ta kara yawar da ta ke takawa a harin da ake kaiwa ta jiragen sama.

A kalamansu na karshe masu wannan taron sun bukaci Mr. Gaddafi ya bar gadon mulki, saboda da shi da gwamnatinsa sun rasa halalci.

XS
SM
MD
LG