Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Al-Shabab Sun Kashe Sojojin Somaliya 20


Sojojin gwamnatin Somaliya akalla 20 su ka mutu guda 18 kuma su ka samu raunuka, bayan da mayakan al-Shabab su ka kai samame a wuni sansanin soji da ke kudancin Mogadishu, abin da kafofin tsaro su ka gaya ma Sashin Somaliyanci na Muryar Amurka kenan.

Majiyoyin sun ce maharan sun tada bama-baman da ke makare cikin wata mota a sansanin sojin El-Salin, sannan su ka danna ciki a harin na asubahin jiya Lahadi.

Maharan sun kwace sansanin na wani dan lokaci, a cewar wani jami’in yankin da ya yi magana da Sashin Somaliyanci na Muryar Amurka.
Mai magana da yawun dakarun Somaliya na musamman ya ce maharan da suka kai hari a sansanin “suna da yawa sosai”.

Mowlid Ahmed Hassan, ya ce fadan ya dauki kusan tsawon minti 40, ya na mai jaddada cewa sojojin sun kare sansanin. Ya ce an tura karin sojojin zuwa sansanin.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG