Titunan birnin Al-Qahira na kasar Masar sun cunkushe a jiya Asabar, yayin da ‘yan sanda suka kakkafa shingayen binciken ababan hawa a sassan birnin.
Daruruwan dakarun kasar dauke da makamai tare da ‘yan sanda sanye da tufafin sulke na kwantar da tarzoma, sun yi ta sintiri a dandalin Tahrir Square.
Dandalin na daya daga cikin wuraren da zanga zanga ta barke a ranar Juma’a, har ila yau wuri ne da ya zama tunga ga masu zangar zangar da suka kai ga kifar da gwamntocin tsoffin shugabannin kasar – Hosni Mubarak da marigayi Mohammed Morsi.
Masu fafutuka, sun jinjina zanga zangar ta ranar Juma’a, inda suka kwatanta lamarin a matsayin budi, bayan da aka kwashe shekaru ana fargabar martanin ‘yan sanda, suka kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da fitowa domin nuna adawa da gwamnatin Shugaba Abdel – Fattah Al- Sissi.