‘Yan sanda a Zimbabwe sun ce shugaban da ke jagorantar likitocin kasar a yajin aikin da suke yi, wanda ake zargin gwamnati ta kama shi, na karbar magani a wani asibiti da ke Harare.
Hukumomin sun kuma ce ba kama shi aka yi ba.
Dr. Peter Magombeyi ya bulla ne a kauyen da ake kira Nyabira da yammacin ranar Alhamis, kwana biyar bayan da aka neme shi sama da kasa ba a gan shi ba
Yayin da ake neman shi, likitoci da sauran ma’aikatan kiwon lafiya sun yi ta zanga zanga, inda suka nemi gwamnati da ta nemo shi, ta kuma tabbatar yana cikin koshin lafiya.
A lokacin watan ganawa da Muryar Amurka, kakakin ‘yan sanda, Paul Nyathi, ya ce Magombeyi na samun kulawa a asibiti.
Ya kara da cewa da zaran an sallame shi, ‘yan sanda za su yi mai tambayoyi.
Magombeyi shi ne mukaddashin shugaban kungiyar likitoci kasar ta Zimbabwe, wanda mambobinta suka shiga yajin aiki a ranar 3 ga watan Satumba.