Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maulidi: Tinubu, Gwamnonin Najeriya Sun Bukaci Gudanar Da Addu’o’in Neman Zaman Lafiya


ABUJA: ANNUR MOSQUE
ABUJA: ANNUR MOSQUE

Sanarwar da mai magana da yawun fadar shugaban kasar, Bayo Onanuga, ya fitar a jiya Lahadi tace, Shugaba Tinubu ya bukaci al’ummar Musulmi suyi amfani da wannan lokaci wajen sake nazari kan kyawawan halaye da koyarwa ta Annabi Muhammad (S.A.W). 

Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin Najeriya sun aike da sakonnin fatan alheri da taya murna ga al’ummar Musulmin kasar akan bikin zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W) na bana.

A cewarsa, “yayin da muke murnar bikin Maulidi, kamata yayi mu sake nazari akan rayuwar annabi Muhammad, wacce ta siffantu da tsarki da sadaukarwa da juriya da kyautatawa da kuma tausayi. Wajibi ne mu siffantu da wadannan kyawawan dabi’u.”

Haka kuma, Shugaba Tinubu ya bukaci al’ummar Musulmin su sadaukar da hutun bikin maulidin wajen gudanar da addu’o’i ga Najeriya tare da nuna tausayi da kauna ga juna.

Haka shima, Gwamna Ahamadu Fintiri na jihar Adamawa, yace wannan lokaci ne da jinsin dan adam ya kamata ya sake duba na tsanaki akansa.

“Na bi sahun sauran al’ummar duniyawajen taya musulmi murnar zagayowar wannan rana mai mahaimmancin gaske kuma na bukaci kowa yayi nazari akan haihuwa da rayuwar annabi Muhammad.”

Ya kuma yi kira ga al’ummar musulmin jihar Adamawa dasu yi amfani da wannan lokaci wajen gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya ga Najeriya, musamman a wannan yanayi na kalubalen tsadar rayuwa. “Mu cigaba da tallafawa gwamnatin jiharmu wajen hidimtawa al’umma, “kamar yadda mai magana da yawun gwamnan, Humwashi Wonosikou ya ruwaito.

A jihar Kogi kuma, Gwamna Usman Ododo cewa yayi, a yayin da al’ummar Musulmin jihar dana sauran duniya ke murnar zagayowa bikin Maulidin ma’aiki na bana, gwamnatinsa ta shirya tsaf domin yin amfani da damar a matsayin hanyar samun karfin da babu rabuwar kannu ko nuna wariya a ciki domin gina jihar Kogin da al’ummarta zasu ci gajiyar hadin kai da taimakon marasa karfi ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG