Kungiyar Ohanaeze mai kare muradun al'umar Igbo ta bayyana matsayinta kan umarnin da kungiyar IPOB ta bayar game da haramta taken Najeriya da cin naman shanu a kudu maso gabashin kasar.
Kakakin kungiyar Ohanaeze Dakta Alex Ogbonnia ya ce, "da hukuma kungiyar IPOB ta ke yi, ba da daukacin alu'mar Igbo ta ke yi ba, saboda a tarukan Igbo muna iya fara taro mu kuma kammala ba tare da rera taken kasa ba."
A cewar Ogbonnia hukuma tana da dama ta bi wannan umurnin ko kuma ta watsar da shi.
Game da batun hana cin naman shanu daga arewacin Najeriya, Ohanaeze ta ce "bin wannan umurnin na ganin dama ne, saboda kana da zabi ko ka saya ka ci naman shanun arewaci ko ka ki yin hakan"
"Akwai mutanenmu Igbo da ke arewa kuma dukanninmu muna musayar kyawawan al'adu da ma hulda da yan arewa. Saboda haka, hana cinikin abin da aka fi sanin wata kabila da shi ba zai amfani al'umar Igbo ba," inji kakakin Ohanaeze, Dakta Alex Ogbonnia.
Mista Celestine Ositadinma wani shugaban al'uma ne, kuma ya yi tir da wannan matakin da kungiyar IPOB ta dauka.
Ya ce, "Ko da yake, kana fafutukar kafa kasarka don cin gashin kai, ba ka da ikon hana taken kasar da kake neman ficewa daga ita. Wannan ba kyakkyawan mataki ba ne wajen samun cin gashin kai. Ba ka hana taken Najeriya har sai ka samu naka kasar da yancin."
"Hana cin naman shanu daga arewa shi ma ba daidai ba ne, saboda ba ka gaya wa mutum abin da zai ci da abin da ba zai ci ba. Kowa yana da zabi anan, kuma wannan ma ba zai taimaka wa fafutukar da suke yi ba." In ji Ositadinma.
Tuni hadakar kungiyar masu fataucin dabbobi da kayan abinci ta kasa ta mayar da martani ta bakin shugaban nata Kwamred Muhammad Tahir.
Yanzu abin jira a gani shi ne tasirin umurnin hana rera taken Najeriya a makarantun kudu maso gabashin Najeriya da ke yankin kabilar Igbo, yayin da za a bude makarantu a mako mai zuwa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: