Tun ba'a yi nisa ba mahalarta taron sun fara sainsa kan batun kudi. Wani Abubakar Sadiq mai sharhi kan harkokin yau da kullum yace hutun mako daya da aka bayar an yi haka ne domin a samu a sawa kowa kudinsa a banki kafin a cigaba da taron. Yace wasu sun kekasa kasa sai an biyasu kudaden da aka ce za'a biyasu.
Bayan shugaban kasa ya yi jawabi ya bayyana abun da za'a biysau sai wasu suka fara cewa komenene za'a biyasu a biyasu kafin tafiya ta yi nisa. Sun bukaci a biyasu da dirbobinsu da ma masu taimaka masu. Sun hakikance a biya kowa hakinsa. Sun ce basa bukatar wata hidima da sauransu.
A kidayar da aka yi an kiyasta kowanensu zai sami akalla nera miliyan goma sha biyu da wasu abu. Amma Pastor Tunde Bakare daya daga cikin wakilan yana ganin babu wanda ya hakikance a biyashi kafin ya cigaba da taron. Yace yawancin mahalarta taron mutane ne dake da abun hannunsu.
Dr Emmanuel Usman Shehu wanda ya janye daga taron yace ya yi haka ne domin ba'a gayyaci mutane yadda ya kamata ba domin yakamata kowace kabila ta samu wakilci a taron. Yace idan za'a yi abu a yi bisa kan tsari domin a tabbatar ba'a bata lokaci ba ko kashe kudi a banza ba.
Ga karin bayani.