Shugaban ma'aikatan kananan hukumomin Najeriya Ibrahim Khalil yace baiwa kananan hukumomi 'yancin cin gashin kansu ne kadai zai ba talakawa ingantacciyar rayuwa da kyautata rayuwar wadanda suke karkara.
Yace gwamnonin jihohi sun fatattaka tsarin kananan hukumomi. Biyan albashi ma yakan yi wuya a wasu wuraren. Yace duk jihar da mutum ya je zai ga an debo kananan ma'aikata an dorasu kan manya. Yace wannan almundahana ce mafi girma wadda ya kamata EFCC ta dinga kalla ba lallai maganar kudi ba kawai. Misali mutumin da aka daukeshi a bangaren aikin noma sai a turashi wurin kasafin kudi.
Inji Ibrahim Khalil suna neman tsare-tsaren da zasu tabbatar da 'yancin kananan hukumomi da hana gwamnoni yi masu karan tsaye a harkokinsu. Gwagwarmayar da suke yi da fadawa duniya ta kafofin gidajen rediyoyin kasashen waje suka sa yanzu mutane sun fara ganewa. Yace ba'a bar masu kananan hukumomi su yi abun da suke so ba. Mutanen da suke karkara, talakawa da wadanda ake ganin su ba komi ba ne su ne da kananan hukumomi.
Manoma, masaka da masu kananan sana'o'i an yi kananan hukumomi ne dominsu. Ba'a yiwa gwamnoni ba. Idan an inganta kananan hukumomi babu dalilin da zai sa mutane suna barinsu zuwa manyan birane.
Mazauna karkara suna bukatan a yi masu hanyoyi domin akwai wasu wurare da zara damina ta sauka to babu hanyar da zasu bi su fita sai bayan wata uku lokacin da damina ta dauke. Wasu kauyuka ma basu da makarantu wadanda suke dasu basu da malamai. Ruwan sha shi n babban damuwa. Sai a samu kwatami inda dabbobi da jama'a ke zuwa neman ruwan sha.
Bisa ga haka shugaban karamar hukumar Pankshin ya bukaci gwamnatin tarayya ta ba kananan hukumomi hakinsu kai tsaye domin su yiwa mutanensu aiki.
Ga rahoton Zainab Babaji.