Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan Fulani Sun Yabawa Shugaba Jonathan


Wasu Matasan Fulani
Wasu Matasan Fulani

Matasan Fulani a Najeriya sun yabawa shugaban kasa Jonathan mai barin gado da kalamun taya Janar Buhari murnar lashe zaben shugaban kasa.

Alhaji Sha'aibu Haruna Sojigi shugaban kungiyar matasan Fulani a Najeriya shi ya bayyana yabawar tasu ga manema labarai.

Yace a gaskiya ya jinjinawa shugaban kasa mai barin gado Goodluck Ebele Jonathan a matsayinsa na shugaban kasa. Shi ya fara bada sanarwar nasarar Janar Buhari. Yace lallai ya nuna mazantaka. Yace kowa ya yi koyi da abun da ya yi. Ya taka babbar rawa.

A nahiyar Afirka shugaba Jonathan ya bude wani babin tarihi. Tun kafin INEC ta bada sanarwar sakamakon zaben ya fito ya amince cewa shi ya sha kaye kuma ya taya wanda ya kayar dashi murna.

Dangane da ko shugaba Jonathan zai garzaya kotu sai Alhaji Haruna yace a yadda ya yi jawabi da wuya ya yadda wani ya rudeshi.

Gameda zaben Janar Buhari Haruna yace tunda aka haifeshi bai taba yin murna irin murna aka zaben Janar Buhari ba.

A wannan karon yace zasu yi tattaki su je su gaida Janar Buhari da zara ya dare kan gadon mulki.

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG