Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Ne Kashin Bayan Kowacce Al'umma


Mata, Maza, Matasa da Dattijai da ma Yara sun fito domin nuna farincikinsu a kan titin Zoo Road Kano
Mata, Maza, Matasa da Dattijai da ma Yara sun fito domin nuna farincikinsu a kan titin Zoo Road Kano

An kira wani babban taron matasa na kasa a Najeriya game da harkokin su da yadda za a biya masu bukatunsu.

Shugaban taron na kasa Hon. charles Olufemi Falayo a loakacin da yake bayanin dalilin da ya sa suka kira baban taro, inda yake bayyana cewa matasa ne kashin bayan kowacce al'umma don suke da kuzarin karfafa tattalin arziki, hazaka da ciyar da kasa gaba.

Ya ce a wannan taron za tattauna yadda makomar matasan Nijeriya za ta kasance. kusan a iya fahimtar cewa 'yan majalisar dokokin matasa ne kan gaba wajen wannan taron.

Matasa da ya wa sun halarci wanna taron inda suka tattauna abubuwan da suka shafesu, da kuma neman hanyar da zasu cimma burinsu kuma suna sa ran a karshen taron za a cimma matsaya.

Abdullahi Aliyu Katsina na daya daga cikin shugabannan matasan Najeriya dake kan gaba wajen gudanar da taron. Malam Abdullahi yace abubuwa biyu ne za a tattauna akansu a taron, na farko shine yadda rayuwar matasa take a yau, na biyu in rayuwar ba ta da kyau wace hanya ce za a bi a inganta rayuwar matasa a yau da nan gaba. Abu na uku shine, akwai kudurori da ake gani ya kamata a fidda a ba gwamnati don ta yi aiki a kansu wanda idan tayi aiki a kansu, yana fata rayuwar matasa zata sami chanji.

XS
SM
MD
LG