Kawo yanzu dubban mutane suka rasa rayukansu musamman a Borno da Yobe. Lamarin sai ya yi kamar ya lafa amma sai kuma 'yan ta'adan su fito da wani sabon salo da ke kara asara rayuka kamar yadda aka gani cikin 'yan watannin nan. Don haka abun yabawa ne cewa alhazan Najeriya, musamman daga arewa, sun gudanar da addu'ar samun zaman lafiya a Najeriya yayin da suke aikin hajjin bana. Jihohin Borno da Yobe su ne suka fi shan azabar tashe-tashen hankula a kasar.
Farfasa Tijjani El-miskin shugaban alhazawan ya yi magana kan alfanun addu'a Ya ce tun da suka dukufa da yin addu'a a Borno abubuwa sun fara kyautuwa domin yanzu jama'a na yawo a cikin garin Maiduguri har zuwa karfe 11 abun da da babu shi kodayake har yanzu akwai fama a kauyuka da karkara inda ana cigaba da kashe-kashe da kone-kone da rushe-rushen gidajen mutane. Ya ce ba gwamnatin tarayya ba hatta duk 'yan adam basu isa su yaye masu masifar da ta addabesu ba sai dai Allah. Abun da Allah zai yi yafi na mutum, ya fi na gwamnatin tarayya kuma ya fi nasarar mutane. Gwamnati na iya kasawa amma Allah ba ya kasawa. Sabo da haka mutane sun dukufa suna ta yin addu'a a Minna kafin su je Arafa. Can ma mutane sun cigaba da yin addu'a. Ya ce suna da tabbacin cewa Allah zai karbi addu'o'in da suka yi. Suna kuma rokon Allah bayan Ya yaye ma kasar matsalar Ya azurtar da kasar, a samu zaman lafiya, a samu jituwa, kasar kuma ta gyaru kamar kasashen da suka cigaba.
Ita ma jihar Zamfara na cikin jihohin dake fama da tashe tashen hankula sanadiyar aika aikar 'yan fashi da makami. Jihar na cikin jihohin da suka yi addu'o'in neman zaman lafiya a Saudiya. Gwamnan jihar Zamfara Yari ya ce suna rokon Ubangji ya ji ya kawar ma kasar Najeriya tashin hankali da ta'adanci da fashi da makami. Yana fata Allah ya hada kan mutanen yankin da ma al'ummar Najeriya gaba daya.
Ga karin bayani.
LABARI: “Akwai cigaban wannan labari, da wasu labaran masu dumi-dumi, da hotuna, da bidiyo, da cikakkun shirye-shiryen mu duk a shafinmu na www.voahausa.com.”