Janar Dambazau mai ritaya, ya fadawa VOA Hausa a cikin wata hira ta musamman cewa kafa runduna ta 7 ta sojojin da aka yi a Maiduguri, ba ita ce zata shawo kan lamarin ba, domin kuwa fadan sari-ka-noke ake fuskanta, ba wai yaki ne na gaba da gaba da abokin gabar da ka san inda yake kuma kana ganinsa ba.
Yace babban matakin da ya kamata gwamnati ta dauka game da mayakan Boko Haram, shine kasafta su daki-daki domin zabtare karfinsu, ta hanyar gano wadanda aka sanya su daukar makamai bisa dole, da wadanda suka shiga a saboda jahilci, da wadanda suke ciki a sa boda talauci, da kuma ainihin wadanda suke yi domin akida.
Janar Dambazau yace kowane daya daga cikin wannan nau'i na mayakan, hanyar takalarsa dabam ce, idan ana son samun nasara.
Ga cikakken bayanin da Janar din yayi...