Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe 'Yan Sanda 4, Aka Raunata 2 A Bauchi


Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Bauchi, Mohammed Ladan
Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Bauchi, Mohammed Ladan

Kwamishinan 'yan sandan Jihar Bauchi, yace 'yan bindigar da ba a san ko su wanene ba sun kashe sufetoci biyu da saje guda da kuma kofur guda

Wasu 'yan bindigar da ba a san ko su wanene ba, sun bude wuta suka kahs e'yan sanda hudu da maraicen alhamis a garin Bauchi.

Kwamishinan 'yan sandan Jihar Bauchi, Mohammed Ladan, yace 'yan bindigar sun yi kwanton-bauna suka far ma 'yan sandan a titin Gombe, da misalin karfe 7, inda suka kashe sufetoci biyu, da saje guda da kuma wani kofur guda. Wasu 'yan sandan su biyu sun ji rauni, kuma ana jinyarsu a wani asibitin da ba a bayyana ba.

Yace 'yan sanda sun ji rauni ma daya daga cikin 'yan bindigar wanda ya yar da makaminsa ya tsere, kuma ana ci gaba da farautarsa. Babu daya daga cikin wadannan 'yan bindiga da ya shiga hannun hukuma har ya zuwa wannan lokaci.

Kwamishinan 'yan sandan yace su na ci gaba da bincike domin gano ko su wanene 'yan bindigar da kuma musabbababin wannan harin.

Wani wanda ya ga wannan lamarin da idanunsa, yace 'yan bindigar sun shafe kusan minti 30 su na musanyar wuta da jami'an tsaro kafin a turo karin dakarun tsaro zuwa wannan wuri. 'Yan bindigar sun riga sun tsere kafin nan.

Ga cikakken bayanin wannan harin da kuma shaidar wadanda suka ga abin a bakin Abdulwahab Muhammad...

'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Sanda Hudu A Bauchi - 2:22
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG