Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Ta Shiga Rudani a Jihar Neja


APC
APC

Jam'iyyar adawa ta APC ta shiga wani rudani a jihar Neja inda har ta kasa gudanar da zaben fitar da shugabanninta na jihar

A jihar Neja jam'iyyar APC ta kasa gudanar da zaben shugabanninta sabili da rudanin da ta shiga.

Rudani da tsoron barkewar tashin hankali suka sa ala tilas aka dage gudanar da zaben da aka shirya gudanarwa ranar Lahadin da ta gabata. Mutane takwas suka fito suna neman kujerar shugabancin jam'iyyar ta jihar Neja.

Kokarin neman yin sulhu ya kawo mugun rudani wurin da aka shirya yin zaben. Sanata Ibrahim Musa shugaban riko na jam'iyyar yace kowa an bashi dama ya tsaya zaben. Lokacin da ake yin bayani kafin a soma zaben ne sai mutane suka fara rikici. Ganin yadda hargitsin ya tashi sai suka ga babu yadda zasu cigaba da shirin zaben, tilas suka dakatar da shi.

Tuni magoya bayan jam'iyyar suka bayyana takaicinsu akan halin rudanin da jam'iyyar ta afka ciki. Usman Musa jigo a cikin jam'iyyar APC a jihar yace abun da ya faru babban abun kunya ne ga 'yan adawa. Yace yadda aka gudanar da zabukan tun daga gundumomi zuwa kananan hukumomi har aka kawo jiha abun kunya ne. A nashi ra'ayin kamata yayi a bar mutane su zabi shugaban da zai yiwa jam'iyyar aiki tsakaninsa da Allah. Yace shi dan takarar kujerar shugaban jam'iyyar ne. Babu wanda ya tuntubeshi a zabi shugaba ta hanyar sasntawa. Yace kamata yayi a zauna a tattauna idan ta kama wasu su janye sai su janye.

Shi ma Umar Sha'aibu yace zaben shugaban bai yi ba. Wai tun lokacin da suke yiwa mutane ragista suka dinga samun matsala domin wasu sai abun da suke so ne za'a yi. Ya kira shugabannin jam'iyyar na kasa su yi bincike kuma su hukunta duk wanda yake da laifi.

Shugaban matasan jam'iyyar na kasa Alhaji Yakubu Lado yace nan gaba kadan za'a sa ranar shirya wani zaben. Yace sun bada hakuri kuma a matsayinsu na shugabanni zasu kai rahoto Abuja su ga abun da za'a yi.Idan ta kama a sake yin wani zabe uwar jam'iyya zata sa rana. Kuma duk wanda Allah ya bashi a hada hannu da shi a yi aiki tare.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG