Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alaqar Sanusi Lamido da Boko Haram


Tsohon Gwamnan Babban Bankin Kasar Sanusi Lamido.
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Kasar Sanusi Lamido.

A kwanakin baya, rahotanni sun nuna cewa ana tuhumar tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi da alaqa da kungiyar tayar da kayar baya da aka fi sani da Boko Haram.

A lokacin da aka kwace masa takardun tafiya wato Fassfo a filin saukar jirgin saman Mallam Aminu Kano, Sanusi Lamido yayi tsokaci akan wannan kazafi.

“Magana ce suka yi ta a kotu, kuma a kotu an tambaye su yaushe aka fara zarginnan, ba bayani. A ina aka fara zargin, ba bayani. Yaushe aka fara alaqar, babu wata magana. Kuma alkalin ya fada a hukuncinsa, yace wannan karyace kawai, babu ma wani abunda ya kawo wannan maganar, banda cewa sun karbi Fassfo, kuma suna neman wata hujja,” inji Mr. Lamido.

Dan asalin Jihar Kano ya kara da cewa a matsayinsa na dan Najeriya, zai cigaba da yin sharhi, da kuma tsokaci akan al-amuran da suka shafi kasa, kamar yadda ya saba tun kafin ya zama gwamnan Babban Bankin Najeriya.

“Ban yi shiru ba a rayuwata, duk abinda ya kamata a yi magana akai, za’a yi magana akai,” inji Mr. Lamido.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG