Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben APC a Taraba Ya Bar Kura Baya


Sanata Aisha Jummai Alhassan Uwar jam'iyyar APC ta jihar Taraba
Sanata Aisha Jummai Alhassan Uwar jam'iyyar APC ta jihar Taraba

Bisa ga duka alamu zaben shugabannin APC a jihar Taraba ya tayarda kura lamarin har yasa wasu 'yan takara suka fice daga wurin zaben.

Zaben fitar da shugabannin APC a jihar Taraba bai yiwa wasu 'yan takara dadi ba har sun fice daga wurin zaben.

Sanusi Maigari wani jigo cikin jam'iyyar ta APC a Taraba yace abun bakin ciki ne domin haka ba zasu shiga zaben ba domin zaben ba zai haifar da da mai ido ba. Takaddama ta taso a wurin zaben har ma sai da aka yi anfani da jami'an tsaro domin a kwantar da tarzoma. Wasu ma 'yan takara sun fice daga wurin zaben.

Barrister M. B. Mustapha tsohon dan takarar gwamnan jihar a karkashin tsohuwar kam'iyyar CPC yana cikin 'yan takarar neman shugabancin jam'iyyar a jihar kuma ya bayyana dalilansa na ficewa daga wurin zaben. Yace suna cikin jam'iyyarsu ta APC sai wasu daga PDP suka ce an yi masu rashin adalci sai suka karbesu cikin APC. Amma wai yau su ne suka tashi zasu koresu su karbe jam'iyyar.

Mr. John Ikenya ya bukaci uwar jam'iyyar ta hana danniyar da ake so a yi masu. Sun roki uwar jam'iyyar ta kawar da zaluncin da ake yi masu.

Amma Aisha Jummai uwar jam'iyyar ta APC a jihar tace ba haka zancen yake ba. Tace an turo wasu ne domin su kawo rudani.

Daga karshe shugaban riko Alhaji Hassan Jika Ardo shi ne aka bayyana ya lashe zaben inda ya yi alkawarin sasantawa da masu korafi.

Ga karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG