Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matan APC Sun Ce A Shirye Suke Su Rike Muhimman Mukaman Siyasa A Najeriya A Zabe Mai Zuwa


Shugaban rikon kwarya na APC Ma Mala Buni, hagu tare da shugaba Buhari, dama (Instagram/Mai Mala
Shugaban rikon kwarya na APC Ma Mala Buni, hagu tare da shugaba Buhari, dama (Instagram/Mai Mala

Jiga-jigan mata mambobin jam’iyyar APC mai multi ciki har da uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari, sun ce suna shirye tsaf don jan ragamar mulki a kasar.

Matan na jam’iyyar APC dai sun bukaci jam’iyyar tasu da ta tabbatar da cewa ta ba mata manya, kuma muhimman kujerunta a dama da su don ci caban kasa saboda irin karfin da mata ke da su zai taimaka wajen samar da makoma mai kyawu ga kasar.

Matan da ke zaman mambobin jam’iyyar APC sun ci gaba da jadada hakan ne baya ga gudanar da wani gaggarumin taronsu a karo na farko a birnin tarayyar kasar Abuja a kwanakin baya-bayan.

Ambassada Fatima Muhammad Goni, shugabar kungiyar Grassroot mobilizers, kuma jagora a kwamitin bin ka’ida da dabaru na taron matan jam’iyyar APC. ta bayyana cewa a shirye suke tsaf don rike mukamin mataimakin shugaban kasa, sakataren gwamantin tarayya, gwamnoni da dai sauransu,domin a dama da su.

Matan dai sun jaddada cewa, yana da matukar muhimmanci a dauki matakai na dogon lokaci da kuma fitar da tsare-tsare da dabaru don tabbatar da cewa mata sun samu karfin tattalin arziki muddin kasar na son a samu ci gaba mai karfi da hada kai ga bunkasar tattalin arzikinta, in ji Zainab Ahmed dake zaman ministar kudde da tsare-tsaren Najeriya.

A nasa bangare, gwamna Abubakar Bagudu, na jihar Kebbi ya bayyana mahimmancin mata a ci gaban kasa ya na mai cewa kamata ya yi a ci gaba da basu hadin kai da mukaman da zam taimaka wajen ciyar da Najeriya gaba.

Mai taimakawa shugaban Najeriya kan kafaffen yada labarai ma zamani, Bashir Ahmed ya bayyana cewa mata na taka muhimmiyar rawa wajen zabe kuma suna da tasiri matuka a jam’iyyar APC shi ya sa ake mu su sauki a bangaren sayen takardar neman takara.

Imam Isma’il da ke zaman shugaban matasa na jam’iyyar APC ma ya jadada mahimmancin gagarumin taron matan jam’iyyar APC wanda aka yi da zimmar zama tsinsiya daya madaurinki daya.

Idan ana iya tunawa, a makon jiya ne jiga-jigan matan jam’iyyar APC suka gudanar da babban taron don kara hada kai da ci gaba ta fannin rike mukaman muhimmai a kasar don kawo sauyi mai ma'ana ga al’umma duba da yadda matan ke kan gaba wajen jefa kuri’a a lokutan zabe.

Batun shigar da mata cikin muhimman mukaman siyasa abu ne da aka yi ta fafutukar samun kari a kai kuma idan ana iya tunawa a shekarar 2006 ne kudirin jinsi na kasa wato National Gender Policy ya samar da wani tsari na tabbatar da cewa an shigar da kaso 35 cikin 100 na matan Najeriya cikin dukan sha’anin mulki don a dama da su.

XS
SM
MD
LG