A wata sanarwa da Kakakin Buhari, Garba Shehu ya fitar, ya ce shugaban, wanda ya yi magana a wajen Taron Kasafin Kuɗi na Afirka wanda aka gudanar a Grande Palais Ephemere da taken: "Kula da harkokin waje da kuma biyan bashi '', ya ce faduwar farashin kayayyaki sanadiyar COVID-19 ya yi illa ga tattalin arzikin duniya wanda ya yi sandiyar raguwar ci gaban wasu kasashe da mawuyacin halin cibiyoyin kiwon lafiya. Ya kuma kuma bukaci sakin alluran rigakafi zuwa nahiyar, wanda har yanzu ke tafiyar hawainiya.
"A kan wannan ne muke neman goyon bayan gwamnatin Faransa tare da tasirin da take da shi a Tarayyar Turai don ba da gudummawa ga kokarin da ake yi na tattara karin albarkatu don bunkasa tattalin arziki musamman ma Afirka domin karfafa jumlar zuba jari ga tattalin arzikinmu.
Wannan tallafin na kudi ya kamata a fadada shi ma ga kamfanoni masu zaman kansu, '' a cewarsa.
Shugaban ya ce ya kamata Tarayyar Turai ta karfafa rarraba maganin rigakafin COVID-19 cikin adalci a cikin kasashen da ke da karamin karfi.
Karin bayani akan: COVID-19, Faransa, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.