Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna So A Gudanar Da Cikakken Bincike Kan Hatsarin Jirgin Janar Attahiru – PDP


Gwamnonin PDP a wani taro da suka yi a Ibadan, ranar 17 ga watan Mayu, (Twitter/@seyiamakinde - PDP)
Gwamnonin PDP a wani taro da suka yi a Ibadan, ranar 17 ga watan Mayu, (Twitter/@seyiamakinde - PDP)

Har ila yau jam'iyyar ta bukaci da a gudanar da bincike, kan hadurran jiragen sojin Najeriya biyu da suka auku a baya-bayan nan.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta nemi da a gudanar da cikakken bincike domin gano abin da ya yi sanadiyyar faduwar jirgin da ya halaka babban hafsan sojin kasar Laftanar Janar Ibrahim Attahiru.

Attahiru ya rasu ne tare da wasu manyan jami’an sojin kasar 10 ciki har da jana-janar a ranar Juma’a, a lokacin da jirginsu ya fadi a kusa da filin tashin jirage da ke Kaduna.

PDP na kira da a gudanar da kwakkwaran bincike kan hatsarin jirgin sojin Najeriya, da ma sauran hadurra biyu da suka auku a baya, wadanda aka yi asarar rayukan jami’ai” Jam’iyyar ta ce a wata sanarwa dauke da sa hannun Sakataren yada labaranta Kola Ologbondiyan.

A watan Fabrairun bana, wani jirgin sojin saman kasar ya fadi a yankin Abuja, dauke da sojoji bakwai – dukkaninsu sun mutu.

Karin bayani akan: Attahiru, PDP, Boko Haram, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Sannan a watan Afrilu, wani jirgin saman sojin kasar da ke kai wa dakarun kasar dauki a yaki da mayaka Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriyar, ya yi batan dabo dauke da sojoji biyu.

Wadannan hadurra da suka auku cikin dan kankanin lokaci kamar yadda sanarwar ta nuna, abin a yi bincike ne akai.

Cikin sanarwar har ila yau, jam’iyyar ta kwatanta Janar Attahiru da saraun jami’an sojin da suka mutu, a matsayin jarumai, “wadanda suka sadaukar da rayuwarsu don kare kasarmu. Wannan hatsari babban abin koma baya ne ga Najeriya.”

“Jam’iyyarmu na taya rundunar sojin Najeriya, iyalan Janar Attahiru da iyalan sauran sojojin alhinin wannan rashi.”

PDP ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya, da su farga tare da yin addu’o’i ga dakarun kasar maza da mata, wadanda suke sadaukar da rayukansu don su kare kasar.

Cikin wata sanarwa da hedkwatar tsaron ta fitar a ranar Asabar, babban hafsan tsaro Janar Lucky Irabor, ya umurci da a kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin hatsarin.

Hedkwatar ta kuma ce jirgin ya sauka ne a filin tashin jirage na kasa da kasa na Kaduna saboda rashin kyawun yanayi.

Rahotanni sun yi nuni da cewa, a filin jirgin rundunar sojin saman Najeriya da ke Kadunar ya kamata jirgin ya sauka.

Tuni an yi jana’izar Janar Attahiru da sauran sojojin 10 a makabartar dakarun Najeriya da ke Abuja a ranar Asabar.

XS
SM
MD
LG