Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakan Tsaron Bukukuwan Sabuwar Shekara a Kasashen Duniya


Jami'an tsaro
Jami'an tsaro

Dubban daruruwan jami’an tsaro da sojoji za a aika birane a fadin duniya, domin su tabbatar da tsaron mutanen da zasu taru domin yin maraba da sabuwar shekarar 2018.

A nan Amurka, jami’an birnin New York sun sanar da cewa zasu yi amfani da tantancewa mai matakai biyu, zasu girke sojoji a saman gine-gine baya ga karnuka na musamman wajen tabbatar da tsaron dandalin Time Square da aka yi kiyasin mutane miliyan biyu zasu hallara domin yin maraba da sabuwar shekara.

A birnin Las Vegas kuma, dogarawan tsaron kasa 300 ne zasu hadu da jami’an ‘yan sanda sama da 1,500 domin samar da tsaro a cibiyar hada-hadar birnin.

Sai kuma can Kudancin nahiyar Amurka, inda a Rio de Janeiro babban birnin kasar Brazil, ‘yan sanda sun shirya jami’an tsaro 12,000 kusan ‘karin kashi 20 cikin 100 na jami’an da aka yi amfani da su a shekarar da ta gabata, ranar jajiberan sabuwar shekara.

A birnin London kuma, jami’an tsaro ne ‘dauke da makamai da karnuka masu yawan gaske zasu kula da bukukuwan da za ayi da kuma tashoshin jiragen kasa na karkashin kasa.

Sai kuma kasar Jamus, inda a duk manyan biranen kasar da suka hada da Berlin da Munich da Hamburg da kuma Cologne suka bayyana cewa za a kara yawan jami'an 'yan sanda a lokacin bukukuwan sabuwar shekara. sun dai ki bayyana karin bayanin matakan tsaron da zasu dauka.

A Afirka, bayan da wani ‘dan bindiga ya kashe akalla mutane tara ranar juma’a a wajen wata Majami’a dake kusa da birnin Alkahira, Jami’an Masar Sunce sun ‘kara matakan tsaro ranar jajiberan sabuwar shekara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG