Hukumomin shirin samar da abinci, da hukumar inganta kiwon lafiya, duka na Majilisar Dinkin Duniya, sun bukaci a samar da damar da zai sa akai ga mutanen kasar Yemen domin basu kayayyakin jin kai.
wanda shine karshen yakin da akayi a kasar.
Suka ce anyo tafiya mai nisa game da ganin karshen wannan yaki da aka yi a Yemen.
Suka ce fadan na kasar Yemen ya haifar da mummunar halin wayyo ni ALLAH da ayyukan jin kai ya shiga a kasar.
Hukumomi suka ce kashi 75 na daukacin jamaar kasarta Yemen suna bukatar ayyukan jin kai.
Cikin wadannan ayyuka ko har da yara da yawan su yakai sama da miliyan 11 wadanda ba zasu iya iya rayuwa ba sai da wadannan kayayyakin jin kai.
Suka ci gaba da cewa yanzu haka a kalla kashi 60 na ‘Yan kasar suna fuskantar matsalar abinci.
Yayin da wasu miliyan 16 na fuskantar matsalar rashin ruwa mai kyau da tsabtataccen muhalli, kana wasu da dama na fuskantar matsalar abubuwan dake da nasaba da kiwon lafiya.
Tun a shekarar 2015 ne kasar ta Yemen ta fada cikn rikici, tsakanin magoya bayan gwamnatin Abdrabbuh Mansour Hadi wanda keda goyon bayan kasashen duniya da kuma ya tawayen Houthi.
Yayin da Kasar Saudi ke jagorantar taron kasashen dake mara wa Shugaba Hadi baya, su kuma yan tawayen Houthi suna da goyon bayan Iran.
Wannan fadan yayi sanadiyyar mutuwar dubban mutane kana wasu ya bar su da rauni iri daban-daban.
Haka kuma samar da kai kayan agaji ya zame wani babban alkakai ga masu bukata.
Abinda MDD ta bayyana da yanayi mafi muni.
Sanarwan na hadin gwiwa ya bayyana cewa ga bisa dukkan alamu lamarin zai kara Kamari.
Facebook Forum