'Yan gudun hijiran wajen su dubu tara da aka kwaso daga kasar Kamaru suna sansanonin 'yan gudun hijira a Yola da garin Fulfure inda suke samu suna murmurewa.
Alhaji Sa'adu Bello jami'in hukumar NEMA, wato hukumar bada agajin gaggawa, ya bayyana matakan da suke dauka saboda inganta rayuwarsu.
Har yanzu ana yi masu tanadin rumfunan kwana saboda 'yan gudun hijiran na cigaba da kwararowa. Duk da kokarin da suke yi ba komi ba ne ya wadatu.
Har yanzu akwai wasu 'yan gudun hujiran dake kan hanya. Wasu ma an jibgesu a kauyen Sawuda inda jami'an Red Cross ke tallafa masu.
Malam Aminu Mai Kano babban jami'in Red Cross yace da zara sun ketara iyaka sun shiga Najeriya sai so soma duba lafiyar jikinsu kafin su gabatar dasu ga hukumar NEMA su cigaba da nasu taimakon. Idan ta kama su kai mutane asibiti suna hakan.
Wasu cikin wadanda aka kwaso sun furta albarkacin bakinsu. Wani daga Maiduguri yace basu san abun da suke ciki ba saboda yadda 'yan Kamaru suka fara fataktakarsu..
Yawancin wadanda aka kwason 'yan asalin jihar Borno ne wadanda hare-haren Boko Haram ya tarwatsa suka fantsama cikin Kamaru.
An samu an mayar da mutane dubu daya Borno to amma ba'a san abun da ya jawo tafiyar hawainiya ba wajen maidasu jihar Borno.
Alhaji Yerima Aliyu jami'in dake kula da mayar dasu jihar Borno dake Yola yace rasuwar mataimakin gwamna jihar wanda shi ne yake kula da mayar da 'yan gudun hijirar Borno ya kawo jinkiri.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.