Akalla mutane 100 ne aka kashe wasu kusan dubu daya kuma suka jikkata cikin kwanaki biyar,na zanga-zangar nuna kyamar gwamnati a Masar.
Akalla mutane ukune aka kashe jiya Asabar,lokacinda ‘Yansanda suka bude wuta kan masu zanga zanga kusa da ma’aikatar harkokin cikin gida a Alkahira.Wasu mutane 22 ne akalla aka bada labarin aka kashe arangamar jiya Asabar a garin Beni Suef,dake kudancin babban birnin kasar.
Ahalin yanzu kuma,shugaba Hosni Mubarak ya nada babban baturen ‘Yansandan ciki Omar Suleiman,mataimakin shugaban kasa,wan nan ne karo na farko da Mubarak ya nada wani mutum kan wan nan mukami.Haka kuma a jiya Asabar, ya nada ministan zirga zirgan jiragen sama Ahmed Shafiq PM,ya ba shi umarnin kafa sabuwar gwamnati.
Da yake magana,dan gwagwarmaya masu hamayya,Mohammed ElBaradai, yace sabbin nade naden basu wadatar ba.A hira day a yi da tashar talabijin ta Aljazeera,ElBaradai wadda yake da lambar yabo ta Nobel,yace masu zanga zanga suna bukatar canjin gwanati,da kawo karshen abinda ya kira mulkin kama kariya.
Masu zanga zanga da babban sauti sai ci gaba da gangaminsu suke a dandalin Tahrir dake birnin Alkahira,da Alexandria,da kuma Suez.
Dubun dubatan mutane ne suka yi kunnen kashi ga dokar hana yawon dare suna ci gaba da neman ganin Mr.Mubarak da yayi shekaru 30 yana mulki ya yi murabus.
Dibar ganima ce babbar mastala da aka fi fuskanta ahalain yanzu.An sami rahotanni daga Alkahira da Alexandria cewa gungun ‘yan-bnaga, suna fasa kantuna da gidaje suna kwasar ganima.A wasu sassan birnin alkahira mutane sun kafa kungiyoyin masu tsaro dauke da makamaki da sanduna domin kare kadarorinsu.
Dubban fasinjoji ne suka makale a tashar jiragen kasar Alkahira saboda sokewa ko jinkirta tashi da saukar jirage.
Sojoji masu sintiri sun killace wurare yawon bude ido,ciki har da babban gidan adana kayan tarihi da dala-dalan dake kasar.