Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Majalisar Dokokin Koriya ta Arewa Zai Jagoranci Tawagar Kasarsa A Wasannin Olympics A Koriya ta Kudu


Wasan Olympics a Koriya ta Kudu
Wasan Olympics a Koriya ta Kudu

Labarin cewa shugaban majalisar dokokin Koriya ta Arewa zai kasance a wasannin Olympics a Koriya ta Kudu da shugaban Koriya ta Kudu da Firayim Ministan Japan su ma zasu halarta, ya sa ana kyautata zaton akwai damar tattaunawar diflomasiya tsakanin kasashen uku tare da tabbacin za'a gudanar da wasannin cikin lumana

Sanarwar da aka bayar a yau Litinin cewa daya daga cikin manyan jami'an Koriya ta Arewa zai hallarci wassannin Olympics da za’a yi a birnin PyeongChang dake Koriya ta Kudu na janyo sa ran cewa za'a samu sasantawar Diflomasiyya tsakanin kasashen biyu. MA'AIKATAR HADAKA TA KOREA TA KUDU ce ta tabbatar da cewa Kim Yong Nam, Shugaban Majalisar Dokokin Koriya ta Arewa shine zai jagoranci tawagar kasar a bikin bude wasannin da za’a yi a ranar Jumma'a.

" Gwamnatin na sa ran wannan ziyarar da manyan jami'an Korea ta Arewa za su kai zata taimaka wajen yin wasan a PyeongChang cikin kwanciyar hankali da lumana tare da dawo da zaman lafiya tsakalin kasashen Koriyan ," a cewar Baek Tae-hyun, mai magana da yawun ma'aikatar hadaka.

Haka nan shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in, da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence, da Firayim Ministan Japan Shinzo Abe duk zasu halarta, lamarin da zai bada damar a gudanar da tattaunawar difilomasiyya a gefen wasannin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG