Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Yakin Rasha Sun Zafafa Hare-Hare A Lardin Idlib A Syria


Jiragen saman kai farmaki na sojan Rasha samfurin Sukhoi Su-25 a lokacin da suke tashi daga sansanin mayakan saman Hmeimim a lardin Latakia na kasar Syria.
Jiragen saman kai farmaki na sojan Rasha samfurin Sukhoi Su-25 a lokacin da suke tashi daga sansanin mayakan saman Hmeimim a lardin Latakia na kasar Syria.

Jiragen saman yaki na Rasha sun zafafa hare-hare a kan Idlib, lardi na karshe dake hannun 'yan tawaye a kasar Syria, a karshen makon nan da ya shige. 'Yan raji da kuma fararen hula a lardin sun ce an kashe fararen hula 16, aka kuma lalata makarantu, asibitoci da kasuwanni.

An kai wadannan hare-hare masu yawa a kan unguwanni da dama na birnin Idlib da kuma wasu wurare a bayan gari, a bayan da 'yan tawaye suka harbo wani jirgin yakin Rasha samfurin Sukhoi-25 ranar asabar, suka kashe matukinsa.

Wani dan jarida mai suna Khattab Al Ahmed dake zaune a Idlib, ya fadawa Muryar Amurka cewa, "Hare-haren jiragen yakin Rasha sun fi maida hankali a kan garin Saraqeb, wanda ya fi kusa da sansanin mayakan sama na Abu al-Duhur wanda sojojin gwamnatin Syria suka kwace a watan da ya shige. Amma a bayan da 'yan tawaye suka harbo jirgin yakin na Rasha, an kara tsanani da kuma yawan hare-haren ta sama aka fadada shi zuwa wasu sassan."

Kakakin fadar shugaban Rasha ta Kremlin, Dmitry Peskov, ya fada litinin cewa Rasha ta kai hare-hare masu kaifi a kan cibiyoyin 'yan tawaye ne kawai a bayan hare-haren da su 'yan tawayen suka kai. Ma'aikatar tsaron Rasha ta sha musanta zargin cewa jiragen yakinta suna auna fararen hula, tana mai cewa suna daukar dukkan matakan da suka kamata na kaucewa mutanen da babu ruwansu a wannan rikici.

Wata kungiyar tawaye mai suna Hayat Tahrir al-Sham, mai alaka da kungiyar al-Qa'ida, ta dauki alhakin harboi jirgin yakin na Rasha ranar asabar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG