Tsohon dan majalisa Dino Melaye da tawagarsa ta da'awar yaki da cin hanci da rashawa sun yi zanga zangar lalle ne shugaba Jonathan ya kori Stella Oduah Ministar Harkokin Zirga Zirgar Jiragen Sama ta Najeriya domin zargin badakalar nan ta sayo motoci masu sulke guda biyu kan zunzurutun kudi har nera miliyan dari biyu da hamsin da biyar.
Tawagar Dino Melaye rike da kalaye dauke da rubuce rubucen kin jinin cin hanci da rashawa ta taru ne gap da babbar sakatariar tarayya dake daura da majalisar dokoki da babban kotun tarayya da ofishin shugaban kasa. Ana zanga-zangar ke nan sai wasu da Dino ya ce 'yan koran gwamnati ne suka shigo lamarin da ya kusa kaiga sassan biyu yin bata kashi da juna.
Wasu da kila 'yan koran gwamnati ne sun ce ya kamata masu zanga zangar su mika kokensu ta hanyar da ta dace. Wato su mika korafinsu ma hukumar dake kula da zirga zirgan jiragen sama ko NCAA a takaice. Wai abun da 'yan zanga zangar suke yi kiyyaya ce ta siyasa kawai tun da majalisa na bincike kan lamarin kuma gwamnati ta san abun dake faruwa. Don haka suna so ne kawai su fitini matar don sun san mace ce. Suna son su tsoratata domin daga baya su zaga ta yagi wani abu ta basu.
Shi Solomon dake kalubalantar masu zanga zangar an ce kila an yi hayarsa ne amma sai ya ce idan da hayarsa aka yi da an ganshi da 'yan gangami. Shi Dino ne aka yi hayarsa. A tambayeshi, ina motoci masu tsada da yake shiga? Amma Dino da ya ari halin yan banga da kokarin kai naushi ya ce ba zasu raurawa ba.
Ministan yada labaru Labaran Makpu ya ce ba zasu mayarda martani ba sai rahoto ya fito.
Ga Adamu El-Hikaya da rahoto.
LABARI: “Akwai cigaban wannan labari, da wasu labaran masu dumi-dumi, da hotuna, da bidiyo, da cikakkun shirye-shiryen mu duk a shafinmu na www.voahausa.com.”