Amincewa da ma'aikatar zirga-zirgar jiragen sama ta yi na kashe dalar Amurka miliyan daya da digo shida ($1.6) ko kwatankwacin nera miliyan dari biyu da hamsi (N250m) bai hana kungiyoyin dake yaki da cin hanci da rashawa kiran Stella Oduah ministar ma'aikatar ta yi murabus ba. Bayan da shugabannin yaki da cin hanci da rashawa irinsu Rotimi Fashakin suka ce ta sauka domin irin wannan zarmiya ke sanadiyar faduwar jiragen sama wani shugaban wata kungiya kuma tsohon dan majalisa Bina Mailayi ya ba ministar sa'o'i arba'in da takwas ta yi murabus. Ya ce ta ajiye aiki domin rashin imani aka yiwa 'yan Najeriya kuma sun yi Allah Ya isa. Kudin da ta kashe ya ce a mayar dasu nan da zuwa ranar Talata. Idan ba'a mayar da su ba zasu fantsama yin zanga-zanga. Ya ce sun san cewa ministar tana kusa da shugaban kasa kuma sun sa ido su ga abun da zai yi.
Wai an sayo motocin ne domin kare lafiyar ministar daga wadanda suke yi mata barazana domin kin jinin sauye-sauyen da ta ke yiwa ma'aikatar. Tun da labarin sayen wadannan motocin masu dan karen tsada ya fito mutane suka fara tofa albarkacin bakinsu to amma abun ya kara tsamari bisa ga irin kalamun da ministar ke yi na cewa shege ka fasa.
Ga Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani
LABARI: “Akwai cigaban wannan labari, da wasu labaran masu dumi-dumi, da hotuna, da bidiyo, da cikakkun shirye-shiryen mu duk a shafinmu na www.voahausa.com.”