ABUJA, NIGERIA -Taken wannan rana da aka ware don wayar da kan al’umma akan ciwon amosanin jini wato sikila na wannan shekarar shi ne “muhimmancin kula da kai ga masu dauke da wannan cuta.”
Ranar 19 ga watan Yuni na kowacce shekara ne kasashen duniya ke bikin ranar cutar sikila ta duniya, wadda da farko Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar a matsayin wani kuduri na yaki da cutar a shekarar 2008.
A yayin da ake ci gaba da aikin fadakarwa game da cutar, kwararrun likitoci a Najeriya na jaddada muhimmancin kula da kuma magance wannan cuta. Dr. Halima Bello Manga, kwararrar likita ce a fannin jini, ta ce fiye da rabin yaran da ake haifa da sikila a duniya a Najeriya ake haifarsu kuma ga shi babu kwararru da suka san kan cutar a kasar.
A Najeriya ana samun masu kamuwa cutar sikila kimanin 150,000 a duk shekara, a cewar Dr. Halima.
Shugabar gidauniyar Impact Sickle Cell, kuma uwa da ta kula da danta da ya yi fama da cutar sikila, Halima Nagado, ta ce ita da maigidanta jinsin jini mai dauke da sikila (AS) suke da shi, shi ya sa suka haifi da mai lalurar. Ta kara da jaddada muhimmancin yin gwajin jinsin jini kafin aure.
Duk da kokarin masana da ma hukumomin lafiya na wayar da kan al'umma, mutane da dama musamman a karkara, na yi wa gwajin jinsin jini kafin aure rikon sakainar kashi wanda ke maida hannun agogo baya wajen kawo karshen cutar sikila a Najeriya.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf.