Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fiye da kananan yara dubu 100 suke mutuwa da cutar sikila


Wani dan yaro
Wani dan yaro

Bincike na nuni da cewa, kimanin kanananan yara dubu dari ne suke mutuwa kowacce shekara ta dalilin cutar sikila a Najeriya

Bincike na nuni da cewa, kimanin kanananan yara dubu dari ne suke mutuwa kowacce shekara ta dalilin cutar sikila a Najeriya.

Bisa ga rahoton, kimanin mutane miliyan biyar suke fama da cutar daga cikin dubu 150 da ake haihuwa da cutar kowacce shekara kuma dari ke rasa rayukansu.

Darektar cibiyar nazarin aikin magani da horaswa ta jami’ar Badun farfesa Adeyinka Falusi ce ta bayyana haka yayin gudanar da ayyukan makon cutar sikila na duniya.

Darektar ta bayyana cewa, Najeriya tafi kowacce kasa a duniya yawan masu fama da cutar sikila, da kuma rashin ingancin harkokin kiwon lafiya da kula da marasa lafiya. Ta kuma yi kira ga gwamnatin Najeriya ta samar da kayan aiki da za a iya tantance kwayar cutar a jinin jarirai domin daukar mataki kan lokaci.

Farfesa Falusi ta kuma jadada bukatar gwada jini da wayar da kan masu shirin aure dangane da yiwuwar haihuwar yara da cutar sikila da kalubalar dake tattare da cutar da kuma hanyar magancewa.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG