Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci, Wasu Masu Ruwa Da Tsaki Sun Bukaci Gwamnati Ta Tallafawa Masu Fama Da Ciwon Sikila A Najeriya


Likita Firdausi Abubakar Baba
Likita Firdausi Abubakar Baba

Likitoci dake kula da masu fama da ciwon amosanin jini da aka fi sani da ciwon sikila sun bukaci gwamnatin Najeriya ta duba lamarin masu fama da ciwon sakamakon karancin kayan aikin kula da su da kuma karancin asibitoci na musamman, da kuma karancin kawararrun likitoci.

Likitocin dai sun bayyana cewa, duba da yadda akasarin masu fama da ciwon ba su da hali kuma kalilan ne ke da halin daukan nauyin kula da lafiyarsu, kamata ya yi gwamnati ta kara bada himma wajen samar da kayan aiki musamman na’urorin gwaje-gwajen toshewan jini da dai sauransu ganin yadda marasa lafiyan ke da yawa a kasar musamman ma arewaci.

Likitocin sun bayyana hakan ne a yayin tattaunawa ta musamman da su a birni Abuja kan hanyoyin rage yawan masu fama da ciwon sikila da kula da masu ciwo a kasar la’akari da alkaluman kididdiga dake nuni da cewa ana haifan yara dubu 100 a duk shekara da ciwon.

A cewarsu ana bukatar na’urorin tacewa da maida jini cikin jikin masu fama da ciwon sikila musamman masu iya aiki da kan su muddin aka tada su, baya ga karin da ake bukata na kwararru da zasu rinka kula da masu ciwon.

Ana bukatar karin asibitoci na musamman, da kula da masu ciwon amosanin jini a yankunan karkara duk da cewa akwai kadan a wasu garurruwa, in ji likitocin.

Haka zalika, kamata ya yi gwamnati ta taimaka wajen rage kudin magunguna ga masu fama da ciwon in ji dakta Firdausi Abubakar Baaba, likita mai kula da masu ciwon sikila.

A hirar shi da Muryar Amurka, Mustapha Aliyu Jibia, daya daga cikin masu fama da ciwon sikila ya bukaci gwamnati ta kula da batun mahimmaancin da basu magunguna kyauta kamar yadda take ba wa masu fama da cutar kanjamau magunguna kyauta.

Mustapha Aliyu Jibia wani dan shekaru 36 mai fama da ciwon sikila
Mustapha Aliyu Jibia wani dan shekaru 36 mai fama da ciwon sikila

A cewar data Fiddausi, ana iya gano ciwon amosanin jinin tun daga lokacin da uwa ke dauke da ciki yanzu saboda ci gaba da aka samu a fannin kiwon lafiya kuma ana iya ganowa tun wuri idan yaro na dauke da ciwon.

Ta kara da cewa a kan iya dasa kwai a cikin mace ta wajen amfani da fasahar zamani, da ake kira IVF wato In-vitro fertilization wanda akasarin lokaci a ke yiwa wadanda ke samun matsalar haihuwa kuma ana iya gwada kwan uwa a yayin wannan aiki don duba lafiya kuma idan aka gano ciwon amosanin jini sai a dakatar da aikin maida kwan ciki.

Bisa ga bayanin likita Fiddausi, kwayoyin hallitun jinin na sauyawa su koma kaman siffan lauje wanda ke jawo raunatan kwayoyin hallitar wanda kuma ya kan zama hanya na kamuya da ciwon amosanin jini.

Ciwon amosanin jini dai ciwo ne da ke addabar mutane musamman a arewacin Najeriya wanda akasarin lokaci ya fi zuwa da karancin jini, ciwon kashi, yawan masassara da dai sauransu kamar yadda likit Fiddausi ta bayyana.

Ana gadon ciwon amosanin jini ne daga iyaye masu dauke da wasu kwayoyin hallita masu siffar lauje kuma an fi samun ciwon tsakanin larabawa da yan asalin nahiyar Afirka, in ji dakta Fiddausi.

Masu ciwon amosanin jini na fama da ciwo daban-daban kama daga ciwon kashi, ciwon kirji, zazzabin cizon sauro da dai sauransu in ji likitoci.

Sauran matsalolin a amosanin jini ke haifarwa sun hada da daukewan numfashi da gajiya da kuma jinkiri wajen girman jiki, ya na kuma sa idanu da fatar jiki su sauya su zama launin ruwan kwai.

Hira da dakta Firdausi Abubakar Baaba kan ciwon amosanin jini.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG