Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masifa Ke Faruwa a Jihar Borno-inji Shehun Borno


Shehun Borno Alhaji Garba El-Kanemi
Shehun Borno Alhaji Garba El-Kanemi

Yayin da zake zantawa da wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda Biu Shehun Borno Alhaji Garba El-Kanemi yace abun dake faruwa a jihar masifa ce.

Shehun Borno yace abun dake faruwa a jihar ta Borno masifa ce sai dai Allah ya kiyaye.

To sai dai yace abubuwan dake faruwa ba a jihar Borno ba ne kawai. Kusan kowace jiha tana da nata matsalar. Idan an je wasu wurare akwai masu fashi da makami. A wasu wuraren kuma barayi ne koina. A wasu wuraren kuma sace mutane a keyi. Kana kuma ga rigingimu tsakanin makiyaya da manoma.

Amma a Borno kungiyar Boko Haram ce ta damu jihar da ta'adanci. Masifa ce Allah ya kawo domin da can babu irin wadannan abubuwa a Borno. Sabili da haka yace zasu gayawa mutanensu Allah ya tausaya masu. Yace zasu cigaba da magana da gwamnati tare da yin addu'a. Malamai ma suna kokari amma ya roki mutanen gari su yi hakuri. Mutanen Borno gaba daya su yi hakuri domin yanzu babu kasuwa, babu asibiti komi ya tsaya cik. Babu makarantu. Gidajen mutane an konesu.

Shehun ya kira jama'a da su cigaba da addu'a da azumi, kada a gaji har Allah ya kawo zaman lafiya.

Dangane da iyayen da aka sace 'ya'yansu Shehun yace ya je yayi masu jaje da basu hakuri da kuma rokon Allah ya dawo masu da 'ya'yansu. Yanzu ma da kasashen waje suka shiga lamarin da yaddar Allah za'a kawo karshensa.

Zancen danganta abubuwan da kungiyar Boko Haram ke yi da addinin Musulunci Shehun yace addinin Musulunci bai ce su yi abun da su keyi ba. Abun da su keyi ba Musulunci ba ne. Wani abu daban ne su keyi.

Batun sake sabunta dokar ta baci Shehun yace zaman lafiya su ke bukata. Idan dokar zata tabbatar da zaman lafiya babu laifi a yi. Yace yana da tabbacin cewa gwamnati ba zata yi abun da zai cuci mutanenta ba.

Daga karshe ya kira 'yan Najeriya su dinga bada labarin munafukai da barayi da masu tada zaune tsaye. Duk inda aka samesu a fadawa mahukunta.

Ga karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG