Karamar hukumar mulki ta Anka na daya daga cikin kananan hukumomun da suka fi fama da kalubalen kai hare-hare a jihar Zamfara, inda alkaluma suka nuna cewa an kashe daruwan mutane, tare da cinnawa garuruwa da dama wuta, lamarin da kuma yayi sanadiyya raba akalla mutane dubu 29 da muhallansu a yankin kadai.
Sarkin Zamfaran Anka, Alhaji Attahiru Ahmad, wanda kuma shine shugaban majalisar sarautu ta jihar ta Zamfara, yayi bayanin yadda tsarin zai kasance.
To sai dai a cewar wani mai sharhi akan lamurran tsaro, Squadron Leader Aminu Bala Sokoto mai ritaya, akwai babban kalubale ga sabon tsarin. Duk da haka dai Sarkin Zamfaran na Anka, yana ganin za’a iya samun nasarar tsarin, ya kuma yi tasiri sosai a yaki da matsalar tsaro a yankin.
Yanzu haka dai runduna ta musamman ta sojin Nigeria, da ta kumshi sojojin sama da na kasa, hadi da jiregen yaki, suna ci gaba da kai hare-hare a maboyar ‘yan bindigar da ke cikin dazuzukan jihar ta Zamfara.
Facebook Forum