Dr. Hassan Bashir Jibrin, yace wannan cuta wacce take kama makogoro da sauran hanyoyin numfashi, idan ba a kula ba, musamman ga wadanda tuni suke fama da wasu larurori shigen cutar sukari, ko hawan jini, kamuwa da wannan cuta mai shigen mura zata iya assasa hali da suke ciki.
Ita ma kasar saudiyya tana bakin kokarinta wajen shawo kan cutar. Al'amarin ya kai har sai da Sarki Abdullahi ya kori ministan lafiya da mataimakinsa da shugaban asibitin sarki Fhd dake Jidda a kokarin gano bakin zaren.
Ga ci gabar bayanin da Dr. Hassan Bashir Jibrin, kan hanyoyin kaucewa wannan cuta, da kuma yadda za a yi jinyarta idan har kaddara ta riga fata.