Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta Zargi China da Neman Tayarda Fitina


Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel daga hanun dama, jakadan Amurka a Singapore ya tarbeshi ranar Jumma'a da isarsa Singapore.
Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel daga hanun dama, jakadan Amurka a Singapore ya tarbeshi ranar Jumma'a da isarsa Singapore.

Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel ne yayi wanan zargi Asabar din nan a fagen wani taron jami'an tsaro a Singapore.

Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel ya zargi China da daukar matakai da zasu haifarda “fitina” a tekun da ake kira na kudancin China.

A cikin wani jawabi da ya gabatar yau Asabar a wani taron jami’an tsaro da ake yi shekara shekara da ake kira "tattaunawar da ake yi Shangri-La" a Singapore, yace Amurka ba zata kawarda kai ba idan aka yi barazana ga tsarin tafiyarda harkokin da al’amura a duniya.

Haka nan kuma, Mr. Hagel yaci gaba da cewa “haka kuma muna adawa ga duk wani kokari daga ko wace kasa na takaita ‘yancin zirga zirga walau na jiragen sama ko na ruwa, na sojoji ne ko farar hula, daga ko wace kasa babba ce ko karama. Amurka ba zata kauda fuska idan ana kalubale ga tsarin tafiyarda harkokin yau da kullum na duniya ba.

Ya zargi China da hana kasar Phillipines shiga wani bangare na tekun kudancin China, a yankinda kasashen biyu suke gardamar iko da wurin.

Ministan tsaron Amurka yace kodashike Amurka bata goyon bayan ko wani bangare a gardama kan iko, duk da haka Amurka tana adawa da ko wace kasa wacce take amfani da matsin lamba, da tursasawa ko barazana wajen nuna ita ta mallaki wurin.
XS
SM
MD
LG