Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Yakin Ruwa Amurka Sun Ceto Bakin Haure a Tekun Meditaraniyan


Wasu jiragen ruwan yaki na Amurka.
Wasu jiragen ruwan yaki na Amurka.

Wannan mataki ya biyo bayan neman doki da jiragen suka samu daga wani jirgin saman yakin kasar Italiya cewa wani jirgin ruwa yana nutsewa.

Jiragen yakin ruwan Amurka sun ceci bakin hauri 282 a tekun meditareniyan bayan da suka sami kukan neman doki cewa wani jirgin ruwa yana kan nutsewa.

Jiragen yakin USS Bataan da USS Elrod sun kaddamar da aikin ceton ne bayanda wani jirgin saman yaki na kasar Italiya ya hango kananan jirage shida daya daga cikinsu yana nutsewa.

Jami’an sojin ruwan Amurka sun fada jiya Asabar cewa jiragen yakin biyu sun ceto mutane daga cikin teku, daga bisani suka taimaka musu da abinci da kiwon lafiya da kuma muhalli.

Jirgin yakin ruwan Baatan ya mikawa jiragen ruwan soja na kasar Malta mutane 277 ranar jumma’a. Wasu biyar kuma wadanda suke bukatar jinya an dauke su zuwa Maltan jiya Asabar.
XS
SM
MD
LG