A jiya jumma ce hukumar ta bada sanarwar daukar matakin, kuma ba a juma ba mutane suka sake tura sakon nata na farko inda take cewa “ba mu tabbatarba, kuma bamu karyata cewa wannan ne sakonmu na farko ba”.Ta aike da sakonne ta dandalin Twitter, wanda masu sha’awa suka sake aikewa mutane har dubu 75.
Masu sha’awar ayyukan leken asiri zasu iya bin aikace aikacen hukumar ta CIA a adireshin twitter @CIA da kuma a Facebook, domin sanin abunda hukumar ta kira ‘samun karin bayanai, da kuma ganin hotuna, nazari kan tarihinta da bayanai sahihi da hukumar ta tattara kan sassa da kasashen duniya.
Haka kuma hukumar ta CIA tace dandalolinta din zasu rika bada bayanai kan gurabun aiki a hukumar, da kuma bayanai kan dakin adana kayan tarihinta.
Shugaban hukumar John Brennan yace da fadada mu’amalarta ta wadannan hanyoyin sadarwa na zamani, hukumar zata yi hulda da jama’a kai tsaye , kuma ta bada bayanai kan gurorinta, da tarihi da kuma wasu ci gaba da ake samu.