Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Sunce Daya Cikin Mata Takwas, Na Da Hatsarin Kamuwa Da Kansa


'Mata sune zaune a filin sallar idi ranar sallah
'Mata sune zaune a filin sallar idi ranar sallah

Kwarru sun bayyana cewar cutar kansar nono na karuwa tsakanin matan Nijeriya. Bisa ga cewar masana, daya daga cikin mata takwas na da hatsarin kamuwa da cutar a tsawon rayuwa.

Kwararru sun bayyana cewar cutar kansar nono na karuwa tsakanin matan Nijeriya. Bisa ga cewar masana, daya daga cikin mata takwas na da hatsarin kamuwa da cutar a tsawon rayuwa.

Bisa ga cewarsu, lissafi ya nuna cewa kansar na kamar kimanin kashi 12.5 na masu mutuwa da cutar a duniya, abinda yasa ta zama cuta ta biyu mafi kisa. Masana sun bayyana cewa, tsakanin 7,000 da 10,000 na sabuwar cutar na kara yaduwa kowacce shekara, kuma kusan kimanin mata 40,000 ake tsamanin mutuwarsu daga cutar idan ba a dauki mataki ba.

Bincike ya nuna cewa mata sun fi fuskantar hatsarin kamuwa da cutar yayinda take tsufa. Wannan na faruwa ne saboda tsofaffi basu iya kula da kansu yadda ya kamata. Wadansu abubuwan dake karawa mace hatsarin kamuwa da cutar kansar nono sune canjin halitan gado, tarihin iyali na mai cutar, manyan nono, da kuma farkon ganin al’ada kafin shekaru goma sha biyu. Sauran sun hada da lattin al’ada bayan shekaru 55, daukar cikin farko bayan shekaru 30, rashin dauka ciki samsam, yawa ko nauyin jiki bayan yankewar al’ada da kuma shan giya
Masana sunce cutar kansar nono karuwa take a Nijeriya, da kuma kasashe da ke kara girma.

Kansa na farawa daga kari (na jiki) ne wanda ke girma daga yaduwar girma a nono. Yana da muhimmanci a sani cewa, ba kowane girma bane kansa, amma kowacce kansa na girma.

Yayinda fannin kansar wurin fitsarin mata, shugaban kungiyar binciken cutar kansa Dr. Femi Olaleye, ya gane cewa daya daga cikin mata goma sha biyu na dauke da hatsarin kamuwa da cutar kansar wurin fitsari ta dalilin girman jiki. Olaleye ya ci gaba da cewa, hanyoyin kamuwa da kansar wurin fitsarin mata ya shafi ma’amalar mata, canji na halitar gado da girman cutar a jikin mutum, wanda ke karuwa ta wurin yawan abokan jima’i a rayuwa, da sauransu.

Yace, “daya daga cikin mata goma sha biyu na dauke da hatsarin kamuwa da kansar a wannan karnin; kuma kowace mace dake yawan jima’i na fiye da hatsarin kama cuta.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG