Manaja mai kula da ayyukan tallafawa rigakafi a Najeriya na Majalisar Tarayyar Turai, Dr. Ayeke Anthony, yace Tarayyar Turai ta kuduri aniyar tallafawa Najeriya wajen rage mace-macen jarirai da yara kanana, da kuma kawar da kwayar cutar nan dake haddasa shan inna, WPV, daga kasar.
Yace an zabi jihohi 24 domin gudanar da wannan aikin, kuma an kasa shi gida biyu. Kashin farko zai ta'allaka ne ga yaki da cutar Polio ko shan inna.
Jihohin da zasu ci moriyar wannan kashin farko sune Gombe, Kebbi, Plateau, Lagos, Ogun, Abia, Akwa-bom, Edo, Cross River.Kashi na biyu kuma zai lashe Euro miliyan 35, sannan za a gudanar da shi ta hannun Hukumar Kiwon Lafiya tun Daga Tushe ta Kasa a jihohi 24 da aka zaba