Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Kimiyya Na Dab Da Shawo Kan Yada Kwayar Cutar Kanjamau


Masu ilimin kimiyya a Afrika sunce suna dab da shawo kan yada kwayar cutar kanjamau. Masu bincike suna nazari kan wani zobe da mace zata yi amfani da shi dake dauke da maganin kashe kaifin kwayar cutar kanjamau da ake kira Dapivirine.

Binciken kwararru ya gano cewa, idan mace tasa zoben dapivirine a gabanta na tsawon wata guda kafin da sake wani, zai rage hatsarin kamuwa da kwayar cutar kanjamau da kashi 27 cikin dari.

An gudanar da binciken ne a kasashen Malawi da Uganda da Afrika ta Kudu da kuma Zimbabwe. An gudanar da binciken ne a kan sama da mata dubu biyu da dari shida tsakanin shekara ta 2012 da 2014.

Wani jami’in binciken kwakwa dan asalin kasar Zimbabwe Felix Mhlanga ya kago wani salon Magana cewa- Akwai bege kan ASPIRE.

Mhlanga yace, akwai bege da yake mun sami wani abin kariya da ya iya hana kamuwa da cututuka uku. Muna kuma da befe da yake idan aka sami kudi, za a iya saffara wadannan zobuna da yawa domin amfani da shi. Mata ne suke kamuwa da galibin cututukan, kasha sittin cikin dari na mata, da sun sami wannan zoben zasu yi amfani da shi, kuma baka bukatar yiwa wadansu bayani. Ba kamar kwararon roba bane da sai kun yi shawara da abokin tarayyarka.

Za a yi na’am da samun ci gaba a yunkurin shawo kan yada kwayar cutar kanjamau a Zimbabwe da sauran kasashen dake makwabta. An yi kiyasin cewa, kashi sittin da tara daga cikin mutane miliyan talatin da hudu dake dauke da kwayar cutar kanjamau a duniya, suna zaune a kasashen Afrika yankin Hamada.

XS
SM
MD
LG