Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gashin Gira Na Daya Daga Cikin Kawa Ta Halittar Dan'Adam


A wani bincike da masana kimiyya da fasaha suka bayyanar, na nuni da cewar akwai wasu abubuwa da suke maida fuska wata abun sha’awa. Da dama mutane kan dauki Ido, Hanci, da Baki a matsayin abubuwan da suke nuna kyau a fuska. Amma sun iya gano cewa dukkan su basu kai ga gashin gira da na sama da kasan ido ba.

Domin kuwa ta girar fuska ne ake iya ganin kyau, haka ana amfani da gira wajen bayyanar da wasu manufofi da mutun ke nufi, na daga su ko muttsuke su, da zai bayyana ma wani cewar wannan abun ba a yar da dashi ba, ko kuwa yazama abun da aka amince da shi. Yanzu haka 'yan-mata da dama kan kashe makudan kudade don ayi musu gira ta kirkire.

Haka suma gashin sama da kasan ido, sukan taimaka matuka wajen kare ido daga wasu miyagu kanana da manyan abubuwa da kan kaima ido farmaki na bazata. A wani bincike da aka gudanar a jami’ar Lethbridge ta kasar Canada, an nunama mutane hoton wasu fitattun mutane 25 da aka cire musu gira, aka kuma nuna musu na wasu fitattu 25 da aka cire musu ido. Kashi 56 sun iya gane wadannan mutane marasa ido, amma kashi 46 basu iya gane marasa gira ba, hakan dai na nuna cewar gira nada matukar tasiri ga hallitar dan’adam.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG