Yau ne mai kanfanin Facebook Mark Zuckerberg ya tofa albarkacin bakin sa dangane da takaddama Tsakani kamfanin wayar hannu na Apple da hukumar FBI inda hukumar ta bukaci kamfanin ya bada damar kutsawa domin daukar bayanai daga wayar mutumin nan da ya kai hari akan mai uwa da wabi a jahar califoniya ta kasar Amurka.
Zuckerberg ya ce muna tausayawa kanfanin apple a wani taro da aka gudanar a birnin Basalona, shugaban ya kara da cewa ya yi Imani da killace bayanan kowane mai amfani da wayar hannu, amma kuma taimakawa gwamnati domin samun bayanan sirri musamman akan harkar ta’addanci abu ne mai da ya kamata.
Nauyin ya rataya a wuyan kowa, duk da cewa a kwai manufofi da dama da suka haramta ba kamfani damar bada bayanan jama’ar da ke amfani da kayan sa, yakamata duk wani yunkuri ko wani abu mai alaka da ta’addanci a shafukan mu ko manhajojin mu, mu kawar da shi domin bai halarta ba.
Takaddamar da ke tsakanin kamfanin Apple da hukumar FBI ta daukin sabon salo, kamfanin watsapp, da twitter, da google da Microsoft ma sun bayyana rashin gogoyon bayan hukumar FBI a fili karara.